Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki

Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki

- Karin kumallo ko kuma kalace wani nau'in abinci ne da yake da matukar amfani ga jikin dan Adam, sai dai ba kowa yake lura da irin muhimmancinsa balle ya maida hankali don zabar irin abincin da ya kamata ace yana ci domin bawa jikin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba.

- Domin sanin nau'in abincin da bai kamata ake ta'ammali da su ba musamman da sunan karin kumallo ne ya sanya yau Legit.ng tayi duba don kawo muku jerin wadannan bayanai masu amfanarwa:

1- Abinci mai dauke da sukari da yawa

Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki
Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki

Kamar yadda masana suka bayyana, cewa da zarar mutum ya farka daga barci kuma ya tsinci kansa a cikin yanayin yunwa, da yawan mutane kan yi yunkurin yin kumallo da duk abinda suka ci karo da shi, wanda aikata hakan ba daidai bane.

Kamar yadda aka sani cin abinci mai dauke da sukari da yawa yana da hadari ga lafiya domin mutum zai kamuwa da ciwon sukari. Har wa yau zaka ga wasu suna da dabi'ar gujewa ko kuma barin yin kumallo baki daya, wasu ma sun dauka abin burgewa ne ko jarumta, yin hakan na da matukar illa kuma barazana ne ga garkuwar jiki.

KU KARANTA: Ba fa kai kadai ka taba kwana a kurkuku ba ni ma nayi – Martanin Gwamnan Plateau ga Jang

Yana da kyau ace mutane suke ziyartar likita domin samun bayanai game da irin abincin da ya kamata ake ci musamman da safe a matsayin karin kumallo.

2- Rage cin abu mai dauke da sinadarin Carbohydrates a matsayin karin kumallo

Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki
Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki

Cin abinci mai dauke da sinadarin carbohydrates yana da amfani amma yana da kyau a rage cin abinci kamar su dankalin turawa (potatoes), mummuki (Bread) musamman irin wanda ake yi na yanzu masu dauke da sukari da yawa, (Couscous da kuma cereals) dukkansu dangogin abinci me masu amfani sai dai yana da kyau ayi musu hadin gambiza da wasu irin abincin ko kuma a rage cin su da safe saboda suna taimakawa wajen karuwar adadin sinadarin dake cikin jinin dan Adam wanda hakan yana da hadari ga lafiyar jiki.

3- Abinci mai nauyi sosai

Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki
Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki

Dakta Ayurve wani kwararren Likitan msanin nau’ikan Abinci ya bayyanawa cewa, cin abinci mai nauyi da safe ba abu ne mai kyau, saboda hakan yana da wahala wajen markaduwa a cikin dan Adam. Ya cigaba da cewa duk abincin da za a ci da safe wanda yake dauke da nama yana da kyau naman a dafa shi sosai maimakon ace soya shi aka yi, domin hakan ne zai zama mafi sauki wajen narkewa a ciki.

Fara cin abinci marar nauyi da safe kamar Abinci mai dan ruwa-ruwa shi ne mafi amfani domin dukkan sassan jikin dan Adam basu dade da fara aiki ba kuma zai taimakawa wajen basu damar gudanar da aikin yadda ya kamata.

4- Soyayyen Nama

Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki
Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki

Nau'in abinci na gaba shi ne Nama amma wanda aka soya, mai karatu zai yi mamakin jin an ambaci Nama, to amma Nama musamman wanda aka soya cinsa da safe yana da hadari ga lafiyar jiki.

Musamman Naman da aka soya na gidajen Abinci wato (Restaurant) domin zaka same su da yawa naman bai soyu ba sannan gashi suna amfani da sinadarin saka dandano a abinci daban-daban wanda amfani da waSu daga cikin sindaran basu da amfani.

5- Gujewa cin Abinci mai sanyi

Yana da kyau ace mutum idan ya tashi da safe ya ci Abinci mai zafi, domin fara cin Abinci wanda yake da sanyi ba abu ne mai kyau ba domin zai iya jawo wa ita uwar jikin damuwa da matsala. Amma da zarar an yi karin kumallo da abu mai zafi tabbas zai taimaka wajen bunkasar jiki da kuma samun karsashi kasancewar safiya ce yanzu injin cikin nasa zai fara aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng