Allah buwayi gagara misali: Kunga tsohuwa mai shekara 70 dauke da ciki wata 6

Allah buwayi gagara misali: Kunga tsohuwa mai shekara 70 dauke da ciki wata 6

- Tabbas mu'ujizojin Allah suna da yawa ga bayin sa

- Wani labari da ya dauki hankalin al'umma da dama a dukkan fadin duniya na wata tsohuwa mai ciki

- Indai har Allah ya sauke ta lafiya, to za ta zama matar da ta haihu da shekaru mafi yawa a duniya

A wani labari mai cike da al'ajabi tare da tabbatar da buwayar Allah, mun samu cewa an samu wata mata mai suna Maria de la Luz a kasar Mexico mai shekaru 70 a duniya da ta ce tana dauke da ciki wata shidda.

Allah buwayi gagara misali: Kunga tsohuwa mai shekara 70 dauke da ciki wata 6
Allah buwayi gagara misali: Kunga tsohuwa mai shekara 70 dauke da ciki wata 6

KU KARANTA: APC ta saki sunayen mutane 77 da za su jagoranci kawar da PDP a Ekiti

Da take zantawa da majiyar mu a garin nata, tsohuwar da yanzu haka take jiran haihuwar dan ta na takwas ta ce ta tabbatar da shigar cikin na ta ne biyo bayan sakamakon hoton cikin da ta yi aka kuma fada mata cewa mace ce za ta haifa.

Allah buwayi gagara misali: Kunga tsohuwa mai shekara 70 dauke da ciki wata 6
Allah buwayi gagara misali: Kunga tsohuwa mai shekara 70 dauke da ciki wata 6

Legit.ng ta samu cewa sai da wasu daga cikin 'ya'ya da jikokin tsohuwar sun nuna rashin jin dadin su game da labarain suna masu cewa kamata yayi ace ta kyale wa yara hakanan ita ta huta.

Yanzu dai kamar yadda muka samu cewa tuni sun kammala shire-shire da likitan ta wanda ya fada mata cewa za ayi mata tiyata a ciro diyar idan lokacin haihuwar ta yayi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel