Rundunar sojojin Najeriya ta 7 dake yaki da Boko Haram a Maiduguri tayi sabon shugaba

Rundunar sojojin Najeriya ta 7 dake yaki da Boko Haram a Maiduguri tayi sabon shugaba

Rundunar sojojin Najeriya ta bakwai dake yaki da Boko Haram a Maiduguri tayi sabon kwamanda mai suna Birgediya Janar Bulama Biu biyo bayan maida shugaban rundunar Manjo Janar Ibrahim Yusuf da akayi zuwa hedikwatar rundunar a garin Abuja.

Da yake mika ragamar rundunar ga sabon shugaban ta, Manjo Janar Yusuf ya bayyana irin nasarar da ta samu a karkashin sa wanda ya hada da fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram daga wuraren da suka rike a da irin su Camp Zero da sauran su.

Rundunar sojojin Najeriya ta 7 dake yaki da Boko Haram a Maiduguri tayi sabon shugaba
Rundunar sojojin Najeriya ta 7 dake yaki da Boko Haram a Maiduguri tayi sabon shugaba

KU KARANTA: PDP ta bada halayyar wanda za ta tsaida takarar Shugaban kasa a 2019

Legit.ng ta samu cewa shi dai sabon shugaban rundunar Birgediya Janar Bulama Biu dan asalin karamar hukumar Biu ne dake a jihar Borno kuma shine shugaban rundunar na takwas tun bayan kafa ta shekara hudu da ta gabata.

A wani labarin kuma, Wasu al'ummar musulmi a jihar Oyo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a ranar Juma'ar da ta gabata sun gudanar da zanga-zangar kin jinin kasar Isra'ila a kan cigaba da mamayar da take yi wa yankin kasar Falasdinawa.

Da yake magana game da musabbabin yin zanga-zangar, shugaban gamayyar kungiyoyin musulmin kuma shugaban kungiyar gidauniyar Al-Qudus Malam Atta Rasheed ya bayyana cewa abun takaici ne yadda kasashen duniya suka zura ido suna kallon rashin adalcin mamayar tun shekarar 1948.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng