Batan-baka-tan-tan: Murnar sako tsohon gwamnan Filato ta lakume rayukan matasa 2

Batan-baka-tan-tan: Murnar sako tsohon gwamnan Filato ta lakume rayukan matasa 2

Akalla matasa biyu ne daga unguwar Tudun Wada dake a karamar hukumar Jos ta Arewa suka rayukan su yayin bukukuwan murnar sako tsohon gwamnan jihar Filato Jonah David Jang daga gidan Yari da babbar kotun jihar tayi.

Kamar yadda muka samu, matasan da suka mutu sun hada da Peter Sirfwang Kefas da kuma Jerry Sunday kuma sun mutu ne yayin da suke gudu da motar bas kafin daga bisani motar ta kwace masu.

Batan-baka-tan-tan: Murnar sako tsohon gwamnan Filato ta lakume rayukan matasa 2
Batan-baka-tan-tan: Murnar sako tsohon gwamnan Filato ta lakume rayukan matasa 2

KU KARANTA: An samu danyen mai a wurare 7 a Arewa

Legit.ng ta samu haka zalika cewa daruruwan matasa ne dai suka fito saman tituna suna murnan sako jagoran siyasar na su Jonah Jang dake zaman Sanata mai wakiltar mazabar jihar ta Filato ta arewa a majalisar dattijai.

A wani labarin kuma, Kamar dai yadda muka kawo maku a jiya cewa binciken da hukumar rukunin kamfanonin albarkatun man fetur na gwamnatin tarayya wata NNPC a gudanar a wasu yankuna a arewa ya haifar da da mai ido bayan da aka gano mai mai tarin yawa a wasu rijiyoyi guda bakwai.

Kauyukyan dai kamar yadda muka samu dukkanin su a cikin jihar Neja suke dake a shiyyar Arewa ta tsakiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng