Koyon sana’ar hannu shine kadai mafita ga matasan Najeriya - Osinbajo
- Mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo, lokacin da ya kai ziyara jihar Kano don kaddamar da makarantar koyon sana’o’In hannu
- Makarantar an kaddamar da ita ne saboda gwamnatin jihar Kano ta tallafawa matasa da sana’o’in dogaro da kai
- Mataimakin shugaban kasar yayi jinjina ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, inda yace wannan hanyace da zata rage talauci a jihar da kasar ma baki daya
Mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo, lokacin da ya kai ziyara jihar Kano don kaddamar da makarantar koyon sana’o’In hannu ga matasa 1000.
Makarantar an kaddamar da ita ne saboda gwamnatin jihar Kano ta tallafawa matasa da sana’o’in dogaro da kai.
Mataimakin shugaban kasar yayi jinjina ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, inda yace wannan hanyace da zata rage talauci da kuma rashin aikinyi a jihar da kasar ma baki daya.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta sanya baki ta nemi kawo karshen yajin aikin ma’aikatar lafiya
Abdullahi Ganduje gwamnan jihar ta Kano, ya bayyana cewa wadanda suka samu wannan horocikin wadanda aka zabo daga kananan hukumomi 44 na jihar, za’a basu tallafin kudi da kuma kayan aiki da zarar sun kamala samun horo daga makarantar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng