Saudiyya ta sake yin raga-raga da makamin 'yan ta'addan Houthi
Tsarin kariya daga barazanonin da suka fito daga sama na Saudiyya,ya tarwatsa wani makami mai linzami da 'yan ta'addan Houthi na Yaman,suka harba wa kasar a daren Alhamis din nan da ta gabata.
'Yan ta'addan sun harba makamin daga Yaman zuwa yankin Najran da ke Kudu maso yammacin Saudiyya,inji kafar yada labarai ta "AL-Akhbariya"
Tashar talabijin "Al Masira" mallakar 'yan Houthi,ta tattabar da faruwar al’amarin,inda ta ce an kai harin ne kan wani sabon sansanin soja da ke yankin.
Hukumokin Saudiyya sun sanar da cewa,ba a yi asarar rai ko daya ba.
Wannan makamin shi ne na 5 a jerin makamai masu linzamin da 'yan shi'ar Houthi suka har wa Saudiyya a farkon watan Ramadan.
KU KARANTA KUMA: 2019: Jam’iyyu sun bullo da sababbin ka’idojin zabe
A nan gida Najeriya kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata, 29 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu.
Hakan ya biyo bayan daidai da ranar tayi na ranar damokradiyar kasar, inda ministan harkokin cikin gida Abdulrahman dan Bazau ya sanar tare da yiwa kasar murnar ranar damokradiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng