Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero ya gurfana gaban EFCC
Hukuma hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC a yau Juma'a, 25 ga watan Mayu, 2018 ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alh Mukhtar Ramalan Yero, domin amsa tambayoyi.
Tsohon gwamnan ya gurfana gaban hukumar ne domin bayyanai kan rawar da ya taka wajen rabe-raben kudin N750 million na yakin neman zabe a shekarar 2015.
Sauran wadanda suka gurfana tare da tsohon gwamnan sune tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Haruna Gaya, da kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar, Hamza Ishaq.
Kamar dai yadda magoya bayan Malam Ibrahim Shekarau sukayi jiya, na Ramalan Yero sun cika ofishin hukumar EFCC suna zanga-zanga.
Yero, wanda da jam'iyyar PDP ne kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar ya zama gwamnan jihar ne a ranan 16 ga watan Disamba sanadiyar mutuwan gwamnan jihar Marigayi Patrick Yakowa a wani mumunaa hadarin jirgin sama.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng