Ko me yayi zafi: Ango ya saki matar sa bayan mintuna 15 da auren su
Wani abun al'ajabi ya faru a kasar daular larabawa, a garin Dubai inda muka samu labarin cewa wani sabon ango ya saki sabuwar amaryar sa kimanin mintuna 15 kacal da daura auren su a gaban alkali.
Kamar dai yadda muka samu, an samu sabani ne a tsakanin angon da kuma surukin sa, uban amaryar a game da yadda za'a biya sadakin amaryar.
KU KARANTA: Rahama Sadau ta yi wa masu sha'awar zama taurari nasiha
Legit.ng ta samu cewa a dai dai lokacin da uban amaryar ya dage kan cewa dole sai angon ya biya sadakin matar a lokaci guda, shi kuma angon ya ce zai biya rabi ne sai bayan amaryar ta tare sannan ya ida cika mata.
Wannan ne dai ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin mutanen har ma da zage-zage kafin daga bisani angon yace ya fasa gaba daya.
Sadakin amaryar dai Dh100,000 ne wanda yake dai dai da akalla Naira miliyan 9,814,000.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng