Hukumar shirya jarabawar JAMB ce za ta yi wa masu son zama 'yan sanda jarabawa
Hukumar rundunar 'yan sandan Najeriya watau Nigeria Police Force (NPF) a turance ta bayyana cewa hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake shirya jarabawar shiga makarantun gaba da Sakandare ta Joint Admission and Matriculation Board (JAMB) ce zata yi wa masu son shiga aikin dan sanda jarabawa.
A cewar hukumar ta 'yan sanda ta kuma bayyana cewa akalla mutane 37,062 da aka tantance ne za su cancanci rubuta jarabawar wanda za'a gudanar da na'ura mai kwakwalwa.
KU KARANTA: An bukaci Buhari ya mika Obasanjo da Jonathan ga EFCC
A wani labarin kuma, Yan majalisar jahar Ekiti da ke a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a yau din nan mun samu labarin cewa sun tsige mataimakin kakakin majalisar Honorable Segun Adewumi bisa zargin sa da sukayi da aikata munanan laifuka.
Haka ma dai duk a zaman majalisar na yau, 'yan majalisar sun kuma tsige mai tsawatarwa a zauren majalisar watau Chif Whip mai suna Akinniyi Sunday tare da maye gurbin sa da Honorable Olawale Onigiobi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng