Abin Murna: Gwamnatin Niger na shirin fara hako mai a jiharta

Abin Murna: Gwamnatin Niger na shirin fara hako mai a jiharta

- Bayan jihar Bauchi da Borno wata jiha a Arewa na shirin fara hakar Man Fetur

- Gwamnatin Niger ta shaida yin duk mai yiwuwa wajen fara tonan Man

- Har ma an bayar da kwangilar fara aikin tona rijiyar man domin sanin adadin yawansa

A yau Alhamis Gwamnatin jihar Niger ta amice da bayar da kwangilar Naira Miliyan N145m domin zurfafa binciken danyan Mai da yake jihar.

Baza a bar mu a baya ba: Gwamnatin Niger na shirin fara hako mai a jiharta
Baza a bar mu a baya ba: Gwamnatin Niger na shirin fara hako mai a jiharta

Kwamishiniyar albarkatun kasa Hajiya Ramatu Mohammed ce ta bayyana haka ga manema labarai a babban birnin jihar Minna.

A cewarta kwararrun da zasu yi aikin sun nemi da a basu Naira Miliyan N381m domin tona rijiyoyin man yayin da suka fara neman mai a jihar. Daga cikin irin wadancan kudade da kwararrun suka nema ne yanzu aka basu N145m. Ramatu ta bayyana.

Sannan ta kara da cewa kwararrun sun yi aiki mai kyau wajen tabbatar da yiwuwar samun danyan man a jihar yayin bincikensu na farko a Kontagora, Kutigi, da kuma Enagi (Bida Basin). Amma yanzu abinda ake son ganowa shi ne yawan adadinsa.

KU KARANTA: Barin zance: Alkali ya umarci wasu ‘yan Jarida su bayyana a Kotu bayan sun tsoma bakin a shari’ar Metuh

Kwamishiniyar ta kuma jaddada cewa tuni Gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da wasu kamfanunuwan ketare guda daga Ingila daya kuma daga Canada kan har kar man.

Da zarar an cimma gano yawan danyan man ya kai yadda ake bukata Gwamnatin jihar zata mikawa Gwamnatin tarayya ragamar cigaba da aikin.

Gwamnatin jihar da ta gabata ce dai ta fara kashe magukudan kudaden har Miliyan N300m wajen ganin an shiga aikin lalubo danyan man a shekara ta 2012 zuwa 2013.

Baza a bar mu a baya ba: Gwamnatin Niger na shirin fara hako mai a jiharta
Baza a bar mu a baya ba: Gwamnatin Niger na shirin fara hako mai a jiharta

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng