Idanun wata Mata sun yi zuru zuru bayan ta yi ma kawarta wanka da tafasashshen ruwan barkono

Idanun wata Mata sun yi zuru zuru bayan ta yi ma kawarta wanka da tafasashshen ruwan barkono

Idanun wata Mata mai suna Uloma Mogaji sun raina fata bayan da ta gurfana gaban Kotu bisa tuhumarta da ake yi da juye ma wata makwabciyarta tafasashshen ruwan barkono a jikinta, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

A ranar ALhamis 24 ga watan Mayu ne aka gurfanar da Mogaji gaban wata Kotun majistri dake Legas, inda ake tuhumarta da cin zarafai da raunata kawartata, sai dai uwargida Mogaji ta musanta tuhume tuhumen duka.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya Musuluntar da Maza 21, Mata 40 daga cikin maguzawan jihar Kano

Dansanda mai shigar da kara, ASP Fidelis Dike ya shaida ma Kotun cewa Mogaji ta watsa ma Happiness da Ekele tafasashshen ruwan barkono da take dafawa akan murhu sakamakon fada da ya barke a tsakaninsu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Fidelis ya bayyana ma Kotu cewa a yanzu haka Ekele na cikin mawuyacin hali, don haka ya roki Kotu ta yi duba da sashi na 171 da 243 na kundin hukunta manyan laifuka ta yanke ma Mogaji hukuncin zaman gidan kaso na shekara daya ko shekaru 14.

Sai dai bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkali Omolaja Kazeem ya bada belin Mogaji akan kudi naira dubu hamsin, tare da mutane biyu da zasu tsaya mata, suma akan kudi naira N50,000. Daga bisani kuma ya dage karar zuwa ranar 27 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng