Kashe Maciji ya sanya Kotu yankewa wani Mutum hukuncin shekara guda a gidan yari
- Wani Mafarauci ya ga ta kansa, bayan da ya kashe wani Maciji
- Yanzu haka zai shafe kwanaki 360 a gidan kurkuku sanadiyyar wannan sheke wani Maciji da yake wahalar samu
- da ma dai ba kowanne irin Maciji ne mahaukuntan yankin suka yarda a farauce su ba
Wata Kotu a kudancin China a garin alkaryar Guangdong ta yankewa wani Mutum hukuncin shekara daya agidan yari a yau Alhamis bisa dalilin kamawa tare da kashe wani Miciji da yake mutukar wahala mai tsayin mita biyu.
Mutumin da aka yanke masa wannan hukuncin da aka bayyana sunan shi da Wu, ya kama katon Micijin ne mai nauyin 10kg a kauyen Fengkai tare da taimakon wani Mutuma da misaln karfe 11:00am na safe a ranar 15 ga wata Disambar shekarar 2016 kamar yadda kotun ta bayyana.
Mutumin mai suna Wu ya karbi kudi har kimanin $47 (300 yuan) sannan ya kama tare kuma da kashe Macijina dai wannan rana.
KU KARANTA: Barin zance: Alkali ya umarci wasu ‘yan Jarida su bayyana a Kotu bayan sun tsoma bakin a shari’ar Metuh
‘Yan sanda sun samu nasarar damke wanann mafaucin Maciji ne bayanda abokinsa ya dora hotonsa a yanaar gizo ta kafar sadarwa ta WeChat, yayinda yake arangamar kama Macijin
Shi kalar irin wancan Macijin yana cikin sahun gaba a cikin jadawalin Macizan da aka hana kashewa kasar. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng