Karanta don sanin dalilin da yasa Jami’ar Al-Qalam ta kori dalibai 16

Karanta don sanin dalilin da yasa Jami’ar Al-Qalam ta kori dalibai 16

- Rashin tarbiyya ya kai wasu dalibai ya baro su

- Jami'ar da suke karatu ta kore su kwata-kwata da karatu a cikinta

- Sannan Jami'ar ta dauki tsauraran matakai kan wasu daliban

Jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina ta kori wasu dalibai da yawansu ya kai har 16 bisa aikata laifukan da suka shafi rashin tarbiyya bayan da hukumar Makarantar ta bayyana cewa laifukan sun sabawa dokokinta karara.

Jami’ar Al-Qalam ta kori dalibai 16 saboda rashin da’a da kuma satar ansar jarrabawa
Jami’ar Al-Qalam ta kori dalibai 16 saboda rashin da’a da kuma satar ansar jarrabawa

Kakakin Jami’ar ne ya bayyan hakan a wani jawabi da ya fitar yau Alhamis. Ya ce daga cikin laifukan da daliban suka aikata sun hada satar amsa, shigar bayyana tsiraici da ikirarin mallakar takardun da ba nasu ba da kuma rashin da’a da sauransu.

Hukumar Makarantar dai ta amince da korar daliban su 16 biyo bayan rahoton da kwamitin ladabtarwa ya gabatar mata.

KU KARANTA: Jagoran ‘Yan Neja-Delta ya zari takobin kare kuri’un Buhari a 2019

Baya ga dalibai 16 da aka kora an kuma dakatar da karin wasu guda 9 har tsawon zagon karatu guda biyu.

Sannan hukumar Makarantar ta sake umartar karin wasu dalibai 29 da su kara nanata zangon karatu har guda biyu, sannan wasu 2 kuma aka mika musu takardar gargadi kada su sake aikata irin laifuka kamar shiga da jaka cikin dakin jarrabawa koda kuwa a gefe suka ajiye.

Majiyar Jaridar Punch ta rawaito cewa shugaban sashin hulda da Jama’a na Jami’ar Mallam Akilu Atiku, ya tabbatar da faruwar lamarin

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng