Da duminsa: Shekarau da Tsohon Minista sun tsallake yin buda baki a kurkuku

Da duminsa: Shekarau da Tsohon Minista sun tsallake yin buda baki a kurkuku

- Tsohon Gwamnan Kano da Tsohon Minista sun shallake kwana a gidan yari, bayan da aka bayar da belinsu

- Wannan gurfanarwa dai ana ganin kamar tana da alaka da sukar da Shekarau yayi ne ga gwamnatin Buhari

- Ana dai zarginsu ne da samun nasu kason daga cikin kudin Makamai da Sambo Dasuki ya rarraba

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan Kano Malam Shekarau da tsohon ministan harkokin waje, Aminu Wali da kuma tsohon kwamishinan Ayyuka na Kano Mansur Ahmed.

EFCC ta gurfanar da Shekarau da wasu mutane biyu gaban kotu bisa zargin halasta kudin haram
EFCC ta gurfanar da Shekarau da wasu mutane biyu gaban kotu bisa zargin halasta kudin haram

Mutane uku dukka sun musanta zargin da ake yi musu har guda 6 daga ciki har da karbar kudi daga hannun jam'iyyar PDP a lokacin zaben 2015 duk da cewa sun sane kudin ba ta halattacciyar hanya suka fito ba.

Hukumar EFCC ce take tuhumar jiga-jigan jam'iyyar ta PDP a Kano da laifuka shida da suka shafi halasta kudin haram da hada kuma hada baki, tuhumar da dukkansu suka musanta.

Mai shari'a Zainab Abubakar Bagi ta babbar kotu da ke unguwar Gyadi-gyadi a birnin Kano bayan kammala sauraron duka bangarorin biyu ta bayar da belinsu.

EFCC ta gurfanar da Shekarau da wasu mutane biyu gaban kotu bisa zargin halasta kudin haram
Aminu Wali - Tsohon ministan harkokin waje

KU KARANTA: Ana zaton wuta a Makera: EFCC ta damke DPO bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan N1.9bn

Wannan tuhuma na zuwa ne kwanaki kadan bayan hirar da BBC suka yi da Malam Ibrahim Shekarau, wanda yake burin yin takarar shugaban kasa a PDP inda a cikin hirar ya caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Magoya bayan Shekarau dai sun ce siyasa ce ta sa aka kama shi, amma gwamnatin tarayya ta sha musanta zargin hakan

Wadanda ake zargin dai sunce an raba kudin ne domin gudanar da ayyukan zabe na jam'iyyar PDP a wancan lokaci kamar yadda uwar jam'iyyar ta kasa ta nemi a yi.

BBC ta rawaito cewa kotun ta cika makil da magoya baya 'yan siyasar, kuma har sai da jami'an tsaro suka harba hayaki mai sa hawaye sannan aka tarwatsa jama'ar da suka taru a wajen kotun lokacin da za a fita su.

EFCC ta gurfanar da Shekarau da wasu mutane biyu gaban kotu bisa zargin halasta kudin haram
EFCC ta gurfanar da Shekarau da wasu mutane biyu gaban kotu bisa zargin halasta kudin haram

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng