Ba fa kai kadai ka taba kwana a kurkuku ba ni ma nayi – Martanin Gwamnan Plateau ga Jang

Ba fa kai kadai ka taba kwana a kurkuku ba ni ma nayi – Martanin Gwamnan Plateau ga Jang

- Da alama Gwamnan Plateau bai ji dadin wata wasika da tsohon gwamnan jihar bayar a karanta a madadinsa ba yayin wani taro ba

- Hakan ya fito fili ne karara a wani martani da ya mayar masa

- Domin a cewarsa kowa yaci ladan kuturu dole yayi masa aski

Gwamnan jihar Plateau Simon Bako Lalong ya tunatar da tsohon Gwamnan da ya gada Jonah David Jang cewa shima fa ya bakunci gidan yarin ja garin Jos kuma har ya shafe kwanaki 40 a cikinsa.

Ba fa kai kadai ka taba kwana a kurkuku ba ni ma nay i – Martanin Gwamnan Plateau ga Jang
Ba fa kai kadai ka taba kwana a kurkuku ba ni ma nay i – Martanin Gwamnan Plateau ga Jang

Gwamna Lalong yayi wannan magana ne a jiya a babban birnin jihar Jos yayinda yake bayani ga Malaman Coci sama da 200 a lokacin gudanar da wani taron kungiyoyin Coci-coci karo na 94, jim kadan bayan wanda ya wakilci David Jang ya gabatar da jawabinsa a wurin taron.

Shi dai David Jang Sanata ne da yake wakiltar Plateau ta Arewa a Majalisar Dattijai ta kasa, kuma ya aiko da sakon fatan alheri ga mahalarta taron. Sannan yace kulle shi da akayi a gidan yari tamkar wani abu ne da Ubangiji ya hukunta don haka kada wani yayi murna ko cewa ya samu nasarar tunkuda shi magarkama. Jawabin da Pastor Abraham Yiljap ya karanta a madadin tsohon Gwamnan.

“A lokacin da nake tsare a Ofishin EFCC na Abuja a kasa na kwana amma sai ga shi a gidan yari na samu darajar kwanciya kan gadon da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya kwanta a lokacin da aka kulle shi a gidan kurkukun na Jos.”

Ba fa kai kadai ka taba kwana a kurkuku ba ni ma nay i – Martanin Gwamnan Plateau ga Jang
Ba fa kai kadai ka taba kwana a kurkuku ba ni ma nay i – Martanin Gwamnan Plateau ga Jang

KU KARANTA: Dandazon al’ummar jihar Kano sun gabatar da sallar Al’kunut a kotu yayinda aka gurfanar da sardaunan Kano (hotuna)

Amma sai dai wancan sako da aka karanta da alama bai yiwa Gwamna Lalong dadi ba, inda ya ware lokaci na musamman domin mayar masa da martini.

A cewarsa shi ma lokacin yana matsayin kakakin Majalisar jihar an kulle shi har na tsawon kwanaki 40. Kuma a karshe aka sake ni.

Haka zalika “Yanzu a matsayi na Gwamna nasan cewa in na sauka tabbas akwai lokacin da nima za’a bukaci na bayar da ba’asi. Amma idan Mutuma ya gaza ganewa cewa shi ajizi ne to doka zata yi aikinta akan shi.” Gwamnan ya bayyana a cikin yanayi mai kama da jirwaye.

Yanzu haka dai kotu zata dawo zama yau domin cigaba da shari’ar da ake yiwa tsohon Gwamnan bisa zarginsa da laifuka har 12 da suka hada da Cin hanci da rashawa da almubazzaranci da dukiyar jama’a da ta kai N6.3b a lokacin yana Gwamnan jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng