Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya yi murabus daga kujeransa
Labarin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu daga majiya mai karfi na nuna cewa mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Nuhu Gidado ya yi murabus daga kujeransa a yau.
Injinya Gidado ya sanar da gwamnan jihar Bauchi, Muhammed Abubakar, ne a wata wasika da ya rubuta tun ranan 16 ga watan Mayu.
A wasikar, Injiniya Gidado ya bayyana cewa dalilin da yasa ya ajiye aikin shine saboda alkawarin da yayi na yin shekaru 4 kacal a gidan gwamnati.
Yace: " Da na karashe wa'adi na, amma bisa ga abubuwan da ke faruwa game da ayyuka na, cigaba da kasancewa a ofishin ba adalci bane gareka a matsayin dan uwana,"
Kana mataimakin gwamnan ya kara da cewa cigaba da zama cutarwa da imaninsa da kuma al'umma.
Bugu da kari, ya tunawa gwamnan ranan 19 ga watan Afrilu cewa yana tunanin ajiye aikina. Injiniya Gidado ya mika godiyarsa ga gwamna Abubakar da kuma al'umman jihar da suka bashi daman bautawa jihar a matsayin mataimakin gwamna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng