Nasarori 4 da na samu tun bayan hawa na mulki - Buhari

Nasarori 4 da na samu tun bayan hawa na mulki - Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya shelanta wasu muhimman nasarori da samu yake kuma alfahari da su a mulkin sa tun bayan zaman sa shugaban kasa a watan Mayu na shekarar 2015 da ta shude.

Shugaban dai yayi wannan kalaman ne lokacin a da yake jawabi a wajen taron karrama wasu zakakuran Najeriya na rukunin National Productivity Order of Merit (NPOM) a turance da ya gudana a garin Abuja.

Nasarori 4 da na samu tun bayan hawa na mulki - Buhari
Nasarori 4 da na samu tun bayan hawa na mulki - Buhari

KU KARANTA: An bukaci Buhari binciki Obasanjo da Jonathan

Legit.ng ta samu cewa shugaban daga cikin abubuwan da ya lissafa, akwai:

1. Yace yanzu kudaden ajiya na kasashen waje a Najeriya sun kai $47 daga $29 a watan Mayu na shekarar 2015.

2. Yace yanzu haka alkaluman tattalin arzikin kasa da ke nuna hauhawar farashin kayan masarufi ya sauka a karo na 15 a jere ya zuwa 12.5.

3. Yace dokar da ya saka ta tattara asusun gwamnati na bai daya ya taimaka sosai wajen toshe dukkan wata kafar da kudade ke zurarewa.

4. Yace gwamnatin da yake jagoranta ta samu nasarar tattala akalla Naira biliyan 120 sakamakon bankadowa tare da korar ma'aikatan boge.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel