Shehunnan malaman addinin kirista sun bukaci Shugaba Buhari yayi murabus
Shehunnan malaman addinin kirista a Najeriya jiya sun bukaci shugaban kasar Najeriya da yayi murabus ko kuma ya tabbatar da samar da kyakkyawan tsaron da zai ba jama'ar kasar nan kariya daga kashe-kashe.
Babban Rabaran din Dakta Martin Uzoukwu da yayi magana a madadin sauran 'yan uwan sa yayin wani gangamin nuna rashin jin dadi game da kisan 'yan uwan su manyan malamai a jihar Benue ya bayyana cewa ba za su lamunci cigaba da kisan na su ba.
KU KARANTA: Kiristoci sun yi wa Buhari zanga-zanga a Abuja
Legit.ng dai ta samu cewa jiya ne dubun dubatar kiristocin kasar nan suka fita saman tituna a manyan biranen Najeriya suna masu zanga-zangar kisan su da suka ce ana yi a kasar nan.
A wani labarin kuma, Shugaba Muhammadu Buhari a jiya ya bayyana cewa kawo yanzu kudaden ajiya na kasashen waje ko baitulmalin Najeriya ya kai akalla $47 biliyan tun 9 gawan Afrilu sabanin $29.6 biliyan din da suka samu kasar a watan Mayu na shekarar 2015.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron karrama wasu zakakuran Najeriya na rukunin National Productivity Order of Merit (NPOM) a turance da ya gudana a garin Abuja.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma
Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng