Ana zaton wuta a Makera: EFCC ta damke DPO bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan N1.9bn

Ana zaton wuta a Makera: EFCC ta damke DPO bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan N1.9bn

- Wani Jami'in tsaro da ya take doka ya shiga komar EFCC

- kuma har an gurfanar da shi gaban Kotu domin fuskantar tuhuma

- Ana dai tuhumarsa ne da laifuka da suka shafi cin hanci da rashawa na makudan Nairori

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da wani tsohon Kwamishinan ‘Yan sanda Victor Onofiok gaban wata Kotu dake zamanta a Apo a garin Abuja a jiya Talata bisa zarginsa da laifuka har 21 da suka hada da wawurewa da karkata akalar wasu makudan kudade.

Ana zaton wuta a Makera: EFCC ta damke DPO bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan N1.9bn
Ana zaton wuta a Makera: EFCC ta damke DPO bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan N1.9bn

Kakakin hukumar Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a wani jawabi, inda ya bayyana cewa, tsohon Kwamishinan yayi aiki ne a Ofishin gudanarwa na rundunar, ta nan ne ya samu damar bayar da kwangiloli ga kamfanunuwansa da kuma bayar wasu kwangilolin ba bisa ka’ida ba.

An dai fara karantowa Tsohon Kwamishinan mai ritaya da yayi aiki a shelkwatar rundunar ‘Yan sanda tsakanin shekarar 2008 zuwa 2009 da cewa; “Kayi amfani da karfin Ofishinka wajen bawa wasu kamfanunuwa Faksene International da Dutse Allah Construction Ventures da Nne-Edak Technical Ventures da Puristic Adherent Company and Quality Watch Construction Company” wadanda mallakarka ne a karkashin kasa kwangiloli ba bisa ka’ida ba da darajar su ta kai Miliyan Casa’in da biyar da dubu dari shida da dubu Saba’in da Naira dari biyar.”

KU KARANTA: 'Yan ta'adda 700 na Boko Haram sun shirya saduda - Gwamnatin Najeriya

Wanda wannan laifi ne da sashi na 12 na kudin aikata laifukan cin hanci da rashawa yayi bayanin hukuncinsa

Amma sai dai bayan karanto masa laifukansa, wanda ake zargin Onofiok ya musanta aikata laifin. Daga nan ne lauyan wand ake kara ya nemi da mai shari’ar da ya amince da bayar da belin tsohon kwamishinan, lamarinda Lauyan EFCC yayi maza ya kalubalanta.

Daga karshe Alkalin Kotun mai shari’a Oji yayi umarni da aci gaba da tsare wanda ake zargin a Ofishin hukumar ta EFCC, sannan ya daga sake zaman don sauraron shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng