Yanzu Yanzu: An sake garkuwa da fasinjoji 42 a Birnin-Gwari zuwa Kaduna

Yanzu Yanzu: An sake garkuwa da fasinjoji 42 a Birnin-Gwari zuwa Kaduna

- A sabon fashi da makami da aka gudanar a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna ‘yan fashi sun sace mutane 42 fasinjojin Kano cikin awowi 24

- Shugaban kungiyar masu safarar mutane na motocin haya (NURTW) na Birnin-Gwari, ya bayyanawa manema labarai cewa lamarin ya auku ne daga yammacin ranar Talata zuwa safiyar ranar Laraba

-An sanar da jami’an tsaro game da aukuwar lamarin sannan kuma ana nan ana kokarin gano mutanen da aka sace sannan kuma a kama wadanda suka sace su

A sabon fashi da makami da aka gudanar a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna ‘yan fashi sun sace mutane 42 fasinjojin Kano cikin awowi 24.

Shugaban kungiyar masu safarar mutane na motocin haya (NURTW) na Birnin-Gwari, ya bayyanawa manema labarai cewa lamarin ya auku ne daga yammacin ranar Talata zuwa safiyar ranar Laraba.

Yanzu Yanzu: An sake garkuwa da fasinjoji 42 a Birnin-Gwari zuwa Kaduna
Yanzu Yanzu: An sake garkuwa da fasinjoji 42 a Birnin-Gwari zuwa Kaduna

Yawancin fasinjojin da aka sace wadanda suka hada da mata yara suna kan hanyarsu ne ta zuwa Kano, lokacin da lamarin ya auku, wasu daga cikin direbobin motocin wadan da suka tsere lokacin da suka hango ‘yan fashi sune suka bayyana haka.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan majalisar jihar Ondo sun ba hammata iska kan mayar da mataimakin shugaban majalisar da aka sauke

PRNigeria ta samu labarin cewa tuni an sanar da jami’an tsaro game da aukuwar lamarin sannan kuma ana nan ana kokarin gano mutanen da aka sace sannan kuma a kama wadanda suka sacesu domin a hukuntasu.

Idan zaku tuna wannan ba shine karo na farko da yan ta'adda ke garkuwa a wannan hanya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel