An damke maigadi dan shekara 63 ya zakkewa 'yar shekara 3
Kotun majista a jihar Kaduna yau Talata ta baa umurnin garkame wani tsoho da shekara 63 mai suna, Olafy Micheal, bisa ga laifin zakkewa yar shekara 3.
Alkalin majistaren, Ibrahim Emmanuel, ya ce a jefa maigadin kurkuku har sai lokacin da aka saurari fatawa daga ofishin hukumar DPP.
Kana ya dakatad da karan zuwa ranan 5 ga watan Yuni domin cigaba da sauraron karan.
Micheal, wanda mazaunin Unguwan Romi a jihar Kaduna ya kasance yana fuskantan zargin lalata da yar karamar yarinya da bata isa aure ba.
Lauyan gwamnati ya bayyanawa kotu cewa DPO na ofishin Sabon Tasha ya mayar da karan ofishin binciken leken asiri domin bincike mai zurfi.
Ya ce Michel ya shigar da yar yarinyar dakinsa inda yayi amfani da yatsunsa wajen lalata da yarinyan.
KU KARANTA: Sanata Omo-Agege da Ali Ndume ya bayyana gaban kwamitin bincike
Yace: "Micheal ya ci mutuncin yarinya yar shekaru 3 ta hanyar sanya yan yatsunsa cikin farjinta. Makwabta ne suka damke shi kuma suka kaishi ofishin yan sanda."
Amma maigadin ya musanta wannan zargi da ake masa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng