Baka tare da mu – Ciyaman na APC ya caccaki ministan Buhari

Baka tare da mu – Ciyaman na APC ya caccaki ministan Buhari

- Ciyaman na jam’iyyar APC na jihar Filato, Latep Dabang, yace ministan wasanni, Solomon Dalung, dan jihar tasu bait aba halartar wani taro ban a jam’iyyar tinda aka bashi wannan matsayi

- Mista Dabang ya bayyana haka a ranar Litinin, a sakatariyar jam’iyyar dake garin Jos, lokacin taron manema labarai, inda ya bayyana al’amuran jam’iyyar

- Ciyaman na jam’iyyar ya kara bayyana cewa Mista Dalung bai halarci taron jam’iyyar ba har guda uku da aka gudanar a kwanakinnan, a jihar

Ciyaman na jam’iyyar APC na jihar Filato, Latep Dabang, yace ministan wasanni, Solomon Dalung, dan jihar tasu bait aba halartar wani taro ban a jam’iyyar tinda aka bashi wannan matsayi.

Mista Dabang ya bayyana haka a ranar Litinin, a sakatariyar jam’iyyar dake garin Jos, lokacin taron manema labarai, inda ya bayyana al’amuran jam’iyyar.

Ciyaman na jam’iyyar ya kara bayyana cewa Mista Dalung bai halarci taron jam’iyyar ba har guda uku da aka gudanar a kwanakinnan, cikin tarukan uku ba wanda ya halarta, har wanda aka gudanar a ranar Asabar data gabata bai halarta ba.

Baka tare da mu – Ciyaman na APC ya caccaki ministan Buhari
Baka tare da mu – Ciyaman na APC ya caccaki ministan Buhari

Ba’a samu ganawa da Dalung ba domin jin abunda zai fada game da zargon da ciyaman na jam’iyyar tasu ta APC ke masa na jihar Filato.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Metuh ya yanke jiki ya fadi ne da gangan - Alkali

A halin da ake ciki, Legit.ng ta ruwaito a baya cewa Justis Okon Abang, na kotun tarayya dake Abuja a ranar Talata, yace tsohon sakataren sadarwa na jam’iyyar PDP Olisa Metuh, ya yanke jiki ya fadi ne da gangan gabanin za’a fara shari’ar a cikin kotun, a ranar Litinin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel