Babban malamin addini zai jagoranci yi wa Buhari zanga-zanga a Abuja

Babban malamin addini zai jagoranci yi wa Buhari zanga-zanga a Abuja

Babban malamin addinin kirista kuma shugaban 'yan darikar Katolika mazauna garin Abuja mai suna John Onaiyekan ya sha alwashin jagorantar dubun dubatar jama'a mabiyan sa domin yi wa shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga.

Kamar dai yadda ya shaidawa manema labarai, zanga-zangar da suka shirya yi wa Buhari din na da nasaba da yadda suka ce yayi wa harkar tsaron kasar rikon sakainar kashi a na kashe kiristoci musamman ma a shiyyar Arewa ta tsakiya.

Babban malamin addini zai jagoranci yi wa Buhari zanga-zanga a Abuja
Babban malamin addini zai jagoranci yi wa Buhari zanga-zanga a Abuja

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya fatattaki 'yan Bet9ja daga jihar sa

Legit.ng ta samu cewa za'a fara zanga-zangar ne daga babbar cibiyar addinin kirista din dake garin Abuja a karfe 10 na safe zuwa babbar cocin Lady Queen a unguwar Garki dukkan su a Abuja, Najeriya.

A wani labarin kuma, Yayin da zabukan shekarar 2019 ke dada kara matsowa, tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo a jiya ya ziyarci hadakar kungiyar hadin kan al'ummar Yarbawa ta Afenifere a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.

Bangarorin biyu dai kamar yadda muka samu sun tattauna ne a sirrance sai dai majiyar mu ta tabbatar mana da cewa abun da suka tattauna bai rasa nasaba da yadda za su hada karfi da karfe waje daya wajen ganin sun hambarar da gwamnatin shugaba Buhari a 2019.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng