Atiku ya karyata cewar ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Filato a gidan yari
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotanni dake cewa ya kaiwa tsohon gwmnan Jihar Filato, Jonah Jang ziyara a gidan yari, ranar Lahadi 20 ga watan Mayu
- Atiku yace shi bai ziyarci Jang ba kamar yadda wasu bangarorin manema labarai sukayi ikirari cewa Atiku ya ziyarci Jang
- Atiku yace duk wadannan labarai basu da asali kuma karya ne kawai an fada ne domin wata manufa da wasu keda ita akansa
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, a ranar Litinin 21 ga watan Mayu, ya karyata rahotanni dake cewa ya kaiwa tsohon gwmnan Jihar Filato, Jonah Jang ziyara a gidan yari.
Atiku yace shi bai ziyarci Jang ba kamar yadda wasu bangarorin manema labarai sukayi ikirari cewa Atiku ya ziyarci Jang a gidan jarum.
Atiku yace duk wadannan labarai basu da asali kuma karya ne kawai an fada ne domin wata manufa da wasu keda ita akansa.
A baya Legit.ng ta ruwaito cewa manyan jagororin jam’iyyar PDP sun ziyarci tsohon gwamnan jihar Filato Jonah jang, a gidan yari na garin Jos.
KU KARANTA KUMA: Mutane na rububin sayen bindigogina daga ko ina a fadin Najeriya - Mai laifi
Sanatan wanda ke fuskantar hukunci game da kudaden da aka diba gabanin saukarsa daga kujerar gwamnan jihar ta Filato, har kimanin N6.3bn.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng