Zaben 2019: INEC zata fara raba katin zabe na din-din-din

Zaben 2019: INEC zata fara raba katin zabe na din-din-din

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbatar da cewa zata fara rarraba katin zabe na din-din-din ga masu su ranar 21 ga watan Mayu.

- Katin zaben dai sai da shi ne ake samun damar yin zabe kamar yadda dokokin hukumar zaben ta kasa ya nuna

Zaben 2019: INEC zata fara raba katin zabe na din-din-din
Zaben 2019: INEC zata fara raba katin zabe na din-din-din

Rahotannin da Legit.ng ta tattara a bayan shafin hukumar ta kafar sadarwa ta Tweeter ya wallafa, ya nuna cewa hukumar zata fara bawa duk wadanda suka yi rijista a shekarar 2017 da wadanda suka bukaci a sauya musu nasu da su je ofishin hukumar na kananan hukumomi dake jahohinsu domin fara karba.

A baya dai mun rawaito muku yadda Sanatan Legas ta tsakiya Oluremi Tinubu tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayar da hutu a ranar 6 ga watan Mayu domin kowa yaje ya karbi katin zaben nasa kafin wa’adin watan Disambar shekarar nan da muke ciki 2018 ya cika.

KU KARANTA: Mai dokar bacci: Kalli hotuna da Bidiyon wasu ‘Yan sandan SARS na shan wiwi da giya

A cewarta katin na PVC shi ne abinda zai ba kowa damar shiga a dama da shi yayin gudanar da zaben shekara ta 2019, a bisa haka ne tayi kira ga duk wadanda suka cika shekarun kada kuri’ar da su tabbata sun karbi nasu katin.

Zaben 2019: INEC zata fara raba katin zabe na din-din-din
Zaben 2019: INEC zata fara raba katin zabe na din-din-din

Hakan na zuwa bayan da hukumar ta INEC ta bayyana cewa akwai Miliyoyin katinan jama’a da har yanzu ba’a karba ba a kasa baki daya wand ajihar Legas take da guda dubu dari hudu da ba’a karba ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel