Idan muka bi abunda Allah yace kasarmu zata canza - Osinbajo
- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, yayi bayanai kan muhimmancin bin maganganun ubangiji sune hanyoyin samun cigaba a kasa
- Osinbajo yace Coci na da muhimmiyar rawa da zata taka wurin gina kasa da kuma samar da cigaba a kasar
- Farfesa Osinbajo ya bukaci mutane da su dage da addu’o’i musamman a wannan lokaci da matasan Najeriya keda bukatar sanin minene cigaban rayuwa
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, yayi bayanai kan muhimmancin bin maganganun ubangiji sune hanyoyin samun cigaba a kasa.
Osinbajo yace Coci na da muhimmiyar rawa da zata taka wurin gina kasa da kuma samar da cigaba a kasar.
Haka zalika mataimakin hugaban kasar ya bayyana cewa Idan har al'umman kasar suka bi dokokin Allah toh babu shakka lamuran kasar zasu daidaita.
Ya bayyana haka ne a lokacin bauta, na Commonwealth of Zion Assembly, dake birnin tarayya, a ranar Lahadi.
KU KARANTA KUMA: Dan Najeriya ya zo na farko a musabakar karantun Al-Qur'ani na Duniya (hoto)
Ya ce: "Idan muka bi abunda Allah yace kasarmu zata canza"
Farfesa Osinbajo ya bukaci mutane da su dage da addu’o’i musamman a wannan lokaci da matasan Najeriya keda bukatar sanin minene cigaban rayuwa.
A halin da ake ciki, Legit.ng ta ruwaito a bayan cewa, jam'iyyar PDP tace shugaba Muhammadu Buhari ya shirya shan kashi a zabe mai zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng