Dakarun soji sun kama manyan yan fashi a jihar Taraba (hotuna)
Rundunar soji karkashin Operation WHIRL STROKE sun yi arangama da manyan yan fashi a jihar Taraba.
Sunyi tawo mu gama da yan fashin ne a lokacin da suke rangajin aiki a jiya a hanyar Manya-Gangun dake karamar hukumar Ussa na jihar inda suka kama mutane 8.
Sun kuma kwato makamai wanda suka hada da bindigogin AK 47 guda biyu, bindigar gargajiya 2, alburjusai, kayan tsafi da wayoyi.
A yanzu haka suna karkashin kulawarsu inda suke amsa tambayoyi.
Sun kuma bukaci al’umma da su sanar da duk wani motsi ko ayyuka da bai yi musu bag a jami’an tsaro mafi kusa.
KU KARANTA KUMA: Buhari zai karbi takardun kasafin kudin 2018 cikin wannan satin - majalisar wakilai
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng