Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi (Hotuna)

Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi (Hotuna)

- Tsohuwar mai suna Fatima mai shekaru 52 ta tara Miliyoyin ne yayin da take bara

- Mabaraciyar dai bata da hannu da kafa, dukkansu dungulmi ne

- Ta rasa hannun nata ne sakamakon yakin basasa da ya afku a kasar ta Lebanon

Abin mamaki baya karewa a duniya, wata tsohuwa mabaraciya ta rasu ta bar Miliyoyin kudi tare tare da karin wasu a cikin asusun ajiya na banki. Har bayan rasuwarta hannunta shanyayyu ne gashi kuma bata iya tafiya.

Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi
Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi

Bayan rasuwarta tane ‘Yan sanda suka gano gawarta a cikin wata tsohuwar Mota a Beirut babban birnin kasar Lebanon, sanann suka gano cewa ashe tana da ruwan kudi haka masu yawa da kuma karin wasu a cikin asusun banki kamar yadda wata takardar ajiyarta ta nuna.

Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi
Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi

Tsohuwar da aka bayyana sunanta da Fatima Othman, ta rasu ta bar kudi kimanin $3,300 a cikin lalitarta da kumakrin wasu Miliyan $1.1m.

Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi
Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi

Kakakin ‘Yan sandan Joseph Musallem, ya shaida cewa Marigayyar ta rasu ne sakamakon bugun Zuciya kuma ba’a zargin ko farmaki aka kai mata.

KU KARANTA: Ma’aikaci ya cizgewa wani dan kasar Indiya hakora 7 saboda bai biya shi albashi ba a Minna

Amma sai dai sunyi mutukar mamakin ganin cewa ta mallaki irin wadannan kudade.

Labarin tsohuwar ya watsu ne tun bayan da wani hoton Soja yana bata ruwa tana sha ya bulla a yanar giza. A sakamakon hakan ne shi ma Sojan kwamandansa ya yaba masa a dalilin halin jin kai da taimakon dan Adam da yayi.

Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi
Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi

Yanzu haka dai jami’an ‘Yan sandan sun mika gawarta bayan sun lalubo dangin Marigayyar a wani gari mai suna Ain Al-Zahab dake Akkar a Arewacin kasar ta Lebanon, kuma har an binne ta.

Abin al’ajabi: Labarin wata Nakasasshiyar Tsohuwa da ta Mutu ta bar Miliyoyin kudi (Hotuna)
Asusun banki kamar yadda wata takardar ajiyarta ta nuna

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel