Karamar magana ta zama babba: An hallaka wani Musulmi saboda ya yanka Saniya

Karamar magana ta zama babba: An hallaka wani Musulmi saboda ya yanka Saniya

Wani matashi, Musulmi mai shekaru 45, Siraj Khan ya gamu da ajalinsa a hannu mabiya addinin Hundu na kasar India sakamakon ya yanka Saniya, kamar yadda wata rahoton gidan talabijin na Channels ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Juma’a, 18 ga watan Mayu, a gundumar Satna dake jihar Madhya Pradesh na kasar India, inda nan take Khan yace musu ga garinku nan, kamar yadda wani jami’in Dansanda Arvind Tiwari ya bayyana.

KU KARANTA: Ba duka aka zama daya ba: Kalli yadda wani Dansanda ke gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani

Haka zalika wani abokin mamacin, Shakeel Maqbool da aka kai musu harin tare, ya sha da kyar, inda a yanzu haka yake jinya raunukan da ya samu a sakamakon harin, a yanzu dai rundunar Yansanda ta aike da jami’anta 400 don gudun barkewar rikici.

Karamar magana ta zama babba: An hallaka wani Musulmi saboda ya yanka Saniya
Masu bautar Shanu

“Mun kama mutane hudu dake da hannu cikin lamarin, kuma mun gano naman Sa da kasusuwan Sa a wajen da aka kashe mamacin, zamu cigaba da bincike don gano musabbabin harin.” Inji Dansanda Tiwari

Su dai mabiya addinin Hindu na bauta ma dabbobi ne, daga ciki har da Shanu, don hake suke yaki da dabi’ar Musulmai na yanka shanu suna cin namansu ko kuwam kiwatasu, wannan ya sanya jihohin kasar da dama suka haramta cin naman Shanu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel