Zaben shugabannin APC: Sanata A'isha Alhassan tasha ruwan duwatsu

Zaben shugabannin APC: Sanata A'isha Alhassan tasha ruwan duwatsu

Da alama dai zabukan shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress, APC da ya gudana a mataki na mazabu, kananan hukumomi da kuma jahohin kasar nan na cigaba da kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin 'ya'yan jam'iyyun.

Kamar dai a jahohi da dama, a jihar Taraba ba mafusanatan matasa sun farfasa tayoyin motar babbar ministan mata a gwamnatin shugaba Buhari kuma tsohuwar 'yar takarar kujerar Gwamnan jihar ta Taraba watau Sanata Ai'sha Alhassan.

Zaben shugabannin APC: Sanata A'isha Alhassan tasha ruwan duwatsu
Zaben shugabannin APC: Sanata A'isha Alhassan tasha ruwan duwatsu

KU KARANTA: Jami'an tsaro a Najeriya sun kama Yahudawa 70

Legit.ng ta samu cewa rahotanni daga jihar Taraba sun rawaito cewa an farfasa tayoyin motar ministar harkokin mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan a yayin rikicin da ya barke tsakanin bangaren jam'iyyar APC wanda take jagoranta a jihar da kuma bangaren wadanda ke adawa da su.

Majiyarmu ta rawaito cewa rikicin ya barke ne biyo bayan jagorantar magoya bayanta da ministar ta yi zuwa wurin da dayan bangaren jam'iyyar APCn ke gudanar da zabe.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng