Tuna baya: Tarihin Likita Mace ta farko a Nahiyar Africa

Tuna baya: Tarihin Likita Mace ta farko a Nahiyar Africa

- Aikin Likitanci aiki ne da ake girmama shi ban komai sai don tsananin wahalarsa da dadewar da ake kafin a kammala shi sannan a zama kwararran Likita, a saboda da haka ne dakiki ko mai matsakaiciyar fahimta baya ma kuskura ya shige shi sama ta ka

Tuna baya: Tarihin Likita Mace ta farko a Nahiyar Africa
Agnes Yewande

Da an yi maganar Likitoci sai Turawa masu jar fata ake fara ake tunawa ba tare da an nazarci tarihi ba don sanin irin gudunmawar da ‘yan gida ‘yan Africa bakar fata suka bayar.

A yau Legit.ng tayi duba na tsanaki ne kan rayuwa da kuma irin gudunmawar da wata ‘yar Najeriya Mace ta farko da ta zama Likita daga Nahiyar Africa ta yamma mai suna Agnes Yewande ta bayar.

Agnes Yewande an haife ta ne garin Edinburg na kasar Scotland a ranar 21 ga watan Fabrairu a shekarar 1906. Kuma tarihi ba zai manta da cewa ita ce Mace ta farko da ta fara zama Likita daga Nahiyar Africa ba tana da shekaru 19 a Duniya.

KU KARANTA: Iko sai Allah: Duba yadda wasu kasashen ke Azumi fiye da awanni 20h kafin buda baki

Agnes Yewande ta samu shiga makarantar Royal College of Music daga nan ta samu tallafin karatu kyauta domin karatu a George Watson’s Ladies College.

Baya ga zama Mace Likita ta farko daga Nahiyar Africa, haka zalika ita ce Mace ta farko da tayi karatun da ya kai matsayin Digiri a shekarar 1929 a lokacin tana ‘ya shekara 23.

Mahaifinta mai suna Richard Akiwande Sr, wanda shi ma Likita ne, ya auri wata baturiya mai suna S. Bowie su biyu Mahaifin su ya haifa da ita da kaninta mai suna Richard Gabriel Akinwande Savage, wanda shi ma ya karanci Likitanci a makarantar Edinburgh University.

Agnes Yewande a lokacin tana Jami’a daliba ce mai mutukar kokari wanda har a shekarar 1929 aka karramata da lambar girmamawa ta Dorothy Gilfillan Memorial Prize a matsayin Macen da tayi fice a cikin daliban da suka fita a shekarar.

Sai dai kuma nasara bata zuwa hakan nan, Yewande ta fuskanci kalubale iri-iri

Kama daga wariyar launin fata da kuma na jinsi yayinda take aiki a God Coast wadda yanzu take a matsayin kasar Ghana.

Tuna baya: Tarihin Likita Mace ta farko a Nahiyar Africa
Tuna baya: Tarihin Likita Mace ta farko a Nahiyar Africa

Mai makon a bata wurin kwana mai kyau a lokacin, sai aka hada ta da bayi tana kwana a cikinsu duk kuwa da cewa ta fi wasu takwarorinta kwarewa a aiki. Daga bisani ta koma aiki da kwalejin Achimota a matsayin malamaa shekarar 1931 har na tsawon shekara 4.

Bisa hazakarta ne shugaban Makarantar Andrew Fraser yayi mata kokarin turawan mulkin mallaka suka karfafeta da aiki mai kyau, ta koma aikinta na Likitanci ta bar Malanta. Daga nan ne ta fara samun albashinta da sauran damarmaki kamar auran tsararta Likitoci.

Haka ta cigaba da samun cigaba har takai matakin shugabantar Asibitin kananan yara dake da alaka da Korle Bu a babban birnin kasar ta Ghana wato Accra.

Daga nan Savage ta kuma shugabanci yunkurin kafa makarantar da horas Ma’aikatan jiyya mai suna Korle-Bu Nurses a shekarar 1947.

Savage ta yi ritaya tare da karasa rayuwarta a kasar Scotland wajen lura da kuma tarbiyyantar da ‘ya’yan kaninta da na kawunnanta, ta kuma mutu a shekarar 1964 a sanadiyyar shanyewar barin jiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng