Iko sai Allah: Duba yadda wasu kasashen ke Azumi fiye da awanni 20h kafin buda baki

Iko sai Allah: Duba yadda wasu kasashen ke Azumi fiye da awanni 20h kafin buda baki

- Inda ranka ka sha kallo, wasu na ganin Azumi na basu wuya ashe akwai kasashen da suke ninka wasu kasashen wajen dadewa ba tare da sunyi buda baki ba.

Musulmai daga Nahiyoyi shida na fadin Duniya na gudanar da Azumi a cikin watan Ramadan. Watan Ramadan wata ne da yake da tsarki a wurin Musulmai kuma suna girmama shi sosai.

Iko sai Allah: Duba yadda wasu kasashen ke Azumi fiye da awanni 20h kafin buda baki
Iko sai Allah: Duba yadda wasu kasashen ke Azumi fiye da awanni 20h kafin buda baki

Amma sai dai awannin da ake gudanar da shi Azumin sun bambanta daga kasa zuwa kasa, wasu kasashen kan yi ‘yan awanni kadan su yi buda baki yayinda wasu kuma kan kusan ninka na wasu kasashen kafin su sha ruwa.

Bayanai dai sun nuna cewa wata kasar na yin Azumi ne na tsawon awa 11 kacal yayin da wata kasar kuma ke yin awanni 21 kafin su sha ruwa.

Kasar da tafi kowacce kasa dadewa bata sha ruwa ba ita ce kasar Iceland, sakamakon masu Azumi a kasar kan shafe har kusan awanni 21 da mintuna 17 (Asuba-2:27am- 10:44pm Magariba).

KU KARANTA: Tsoffin Gwamnoni da Mataimakansu 21 da suke karbar Albashi har sau biyu

Kasar Finland da Greenland sune na biyu wajen dadewa basu sha ruwa ba, domin su kanyi awanni 19 19:25 da kuma 19:21 kowannensu.

Iko sai Allah: Duba yadda wasu kasashen ke Azumi fiye da awanni 20h kafin buda baki
Iko sai Allah: Duba yadda wasu kasashen ke Azumi fiye da awanni 20h kafin buda baki

Haka zalika kasar da kuma tafi kowacce kasa karancin awanni cikin Azumin wannan shekarar ita ce kasar Chile domin kuwa suna Azumi ne na awanni 10 da mintuna 33 kacal, kwatankwacin rabin na kasar Iceland.

Iko sai Allah: Duba yadda wasu kasashen ke Azumi fiye da awanni 20h kafin buda baki
Tutar Chile

Ragowar kasashen kuma da suke yin Azumin kasa da wanni 12 sun hada da: New Zealand awanni 11 da mintuna 35 da kasar South Africa awanni 11 da mintuna 47.

Kasar Brazil da Australia su suka zo na hudu a karancin dadewa basu sha ruwa ba, domin sukan yi awanni 11 da mintuna 59 ne dai-dai.

Yayinda hadaddiyar daular Larabawa suke yin awanni 14 da mintuna 52 bisa lissafin (Khaleej Times).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel