Ba kanta: Ana rigimar kan iyaka tsakanin jahohin 2 a Arewa
Mataimakan gwamnonin jahohin Zamfara da kuma Sokoto dukan su da ke a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya kuma masu makwaftaka da juna sun jagoranci gudanar da wani muhimmin taro da nufin warware takaddamar kan iyakar su.
Taron dai wanda ya gudana a garin Sokoto ya samu halartar jami'an gwamnatocin jahohin da ma kuma hukumar kula da kan iyakoki ta gwamnatin tarayya.
Legit.ng haka zalika ta samu cewa mahalarta taron shawarci al'ummomin yankunan da ake takaddamar kan su da su kai zuciya nesa tare da rungumar zaman lafiya tsakanin su.
A wani labarin kuma, Hukumar rundunar 'yan sanda a Najeriya ta shaidawa 'yan Najeriya wanzuwar wata dokar da ke zaman sabuwa a gare su da ta basu damar su fara cacike dukkan jami'in dan sandan da ya bukaci ya cacike su yayin da yake wani bincike.
Hukumar ta 'yan sandan dai ta shelanta hakan ne a shafin su na dandalin sadarwar zamani na Tuwita mai adreshin @PoliceNG a ranar Alhamis din da ta gabata a kokarin da take yi na wayar wa da al'umma kai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng