Gwamnatin tarayya ta kwacewa Sanata kadarorin ta na Naira biliyan 20
Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da harkokin kadarori da kuma bashi a Najeriya watau Asset Management Corporation of Nigeria a turance ta sanar da karbe kamfanonin Sanata Stella Oduah-Ogiemwonyi.
Kamar dai yadda muka samu, hukumar ta bayyana cewa ta karbe kamfanonin ne saboda tsabar bashin da suka tara da ya kai darajar Naira biliyan 20.
KU KARANTA: Zuwan Buhari tafsir ya yawo ce-ce-ku-ce
A wani labarin kuma, Majalisar tattalin arziki a Najeriya watau National Economic Council (NEC) ta ce akalla zunzurutun makudan kudaden da suka kai Naira tiriliyan takwas ne suka zurare daga manyan ma'aikatun dake tara kudade ga gwamnatin tarayya su kusan 16 daga shekarar 2010 zuwa 2015.
Ma'aikatun dai kamar yadda muka samu sun hada da NNPC, Kwastam, hukumar tashoshin ruwa, hukumar tara haraji ta kasa, hukumar tashoshin jiragen sama da dai sauran su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng