Zuwan Shugaba Buhari tafsir ya jawo ce-ce-ku-ce

Zuwan Shugaba Buhari tafsir ya jawo ce-ce-ku-ce

'Yan Najeriya yanzu haka dai suna ta ci gaba da bayyana mabanbantan ra'ayoyinsu daban-daban game da wasu hotunan Shugaban Kasar Muhammadu Buhari da hadiman sa suka fitar lokacin da ya ke sauraron tafsirin Al-qur'ani mai girma a fadarsa da ke garin Abuja, babban birnin tarayya.

Mun samu cewa dai a ranar Alhamis din da ta gabata ne dai fadar shugaban ta yada hoton a shafukan sada zumuntar ta.

Zuwan Shugaba Buhari tafsir ya jawo ce-ce-ku-ce
Zuwan Shugaba Buhari tafsir ya jawo ce-ce-ku-ce

KU KARANTA: An bankado badakalar tiriliyan 8 a gwamnatin tarayya

Legit.ng ta samu cewa sai dai hakan ya ja hankalin al'ummar kasar sosai biyo bayan wallafa hotunan musamman ma a shafin sadarwar zamani na Facebook.

Wasu daga cikin talakawan kasar dai suna ganin cewa halartar tafsirin tare da yada hotunan sa siyasa ce kawai ganin cewa zaben shekarar 2019 na kara karatowa.

A dayan bangaren kuma, magoya bayan shugaban suna ganin hakan bai da alaka da siyasa sannan kuma suna ta kara yaba masa da kuma yi masa addu'ar samun nasara da karin lafiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng