Sojoji sunce zargin da Danjuma yake yi akan kisan da akeyi a jihar Taraba bashi da tushe

Sojoji sunce zargin da Danjuma yake yi akan kisan da akeyi a jihar Taraba bashi da tushe

- Hukumar Sojin Najeriya a ranar Juma’a tace zargin da tsohon janar T.Y Danjuma yakewa hukumar na cewa ta hada kai da ‘yan ta’adda a Taraba taki ta kare mutane ba gaskiya bane

- Shugaban hukumar sojin Lt. Gen. Tukur Buratai, ya sanar da haka a taron manema labarai a birnin tarayya, inda ya bayyana kwamitin da hukumar ta kafa domin binciken lamarin

- Kwamitin wanda ya kunshi tsofaffin sojoji da kuma wadanda ke cikin aiki da kuma wakilai daga hukumar kare hakkin dan adam ta kasa (NHRC), da kuma kungiyar wayayyu kasa (CSOs)

Hukumar Sojin Najeriya a ranar Juma’a tace zargin da tsohon janar T.Y Danjuma yakewa hukumar na cewa ta hada kai da ‘yan ta’adda a Taraba taki ta kare mutane ba gaskiya bane.

Shugaban hukumar sojin Lt. Gen. Tukur Buratai, ya sanar da haka a taron manema labarai a birnin tarayya, inda ya bayyana kwamitin da hukumar ta kafa domin binciken lamarin.

Kwamitin wanda ya kunshi tsofaffin sojoji da kuma wadanda ke cikin aiki da kuma wakilai daga hukumar kare hakkin dan adam ta kasa (NHRC), da kuma kungiyar wayayyu kasa (CSOs), an kafashi a ranar 10 ga watan Afirilu. Ya kuma bayar da rohoton bincikensa a ranar 25 ga watan Afirilu.

Sojoji sunce zargin da Danjuma yake yi akan kisan da akeyi a jihar Taraba bashi da tushe
Sojoji sunce zargin da Danjuma yake yi akan kisan da akeyi a jihar Taraba bashi da tushe
Asali: Depositphotos

A ranar 24 ga watan Maris, a taron bikin yaye dalibai na jami’ar jihar taraba dake Jalingo, ya zargi wasu sojin najeriya dake aiki a jihar Taraba da hada kai da filani da kuma ‘yan ta’adda wadanda suka kai hari a kauyukan jihar.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ban aje aiki a gwamnatin Jonathan ba - Okonjo-Iweala

Yace sojojin sun kasa kare mutanen kauyukan daga hare-haren da ‘yan ta’addan ke kai masu a garuruwan nasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng