Babu dan adawan da zai iya kada Buhari har yanzu – Kakakin tsohon shugaba kasa
Kakakin tsohon shugaban kasan, Marigayi Umaru Musa Yar’adua, Mista Segun Adeniyi, jiya ya bayyana cewa har yanzu shi bai ga wani dan adawan da ke da karfin kayar da shugaba Muhammadu a zaben 2019 ba.
Adeniyi ya bayyana hakan ne a taron dubin littafin da ya wallafa: ‘Against the Run of Play’ a makarantan ilimin gwamnati da ke Ibadan.
Adeniyi ya siffanta jam’iyyun adawa a matsayin abu mafi muhimmanci da zai isa sanyawa a kayar da gwamnati mai cia fadin duniya. Ya yi waiwayen cewa dalilin da yasa Jonathan ya sha kasa a zaben 2015 shine jam’iyyun adawa sun hada karfi da karfe wajen yakan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Yayinda ake shirin zaben 2019, dan jaridan y ace shi har yanzu bai ga wani dan adawa mai karfi wanda zai iya kayar da Buhari ba saboda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi karfi sosai shekara 1 kafin zaben 2019 kuma a yanzu babu wani jam’iyyar adawa da ta shirya.
KU KARANTA:
Yace: “Ban zaton ganin wani canji a zaben 2019. Ina dai kyautata zaton hukumar gudanar da zabe na kasa INEC ta kara kokari fiye da yadda tayi a zaben 2015. Kuma ina sa ran duk wanda ke son zama shugaban kasa, ya kalubalanci yadda za’a gudanar da zaben.”
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng