Gwamnatin kasar Amurka ta kira Shugaban kasar Najeriya a waya, sun yi muhimmiyar fira

Gwamnatin kasar Amurka ta kira Shugaban kasar Najeriya a waya, sun yi muhimmiyar fira

Babban Sakataren kasar tarayyar Amurka Mista Mike Pompeo ya kira shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a waya inda kuma ya kara jaddada cikakken goyon bayan sa da na kasar su ga shugaban da kuma Najeriya.

Mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar a Najeriya Heather Nauert ita ce ta bayyana hakan ga manema labarai inda kuma tace kasar ta Amurka ta yi jinjina ga shugaban kasar musamman ma game da irin salon mulkin sa da kuma kyakkyawan jagorancin da yake yi a nahiyar Afrika baki daya.

Gwamnatin kasar Amurka ta kira Shugaban kasar Najeriya a waya, sun yi muhimmiyar fira
Gwamnatin kasar Amurka ta kira Shugaban kasar Najeriya a waya, sun yi muhimmiyar fira

KU KARANTA: Osinbajo yayi barazanar yin murabus

Legit.ng ta samu haka zalika cewa jami'in gwamnatin na Amurka ya kira shugaba Muhammadu Buhari din ne a ranar Alhamis din da ta gabata ne, 17 ga watan Mayu.

A wani labarin kuma, Majalisar tattalin arziki a Najeriya watau National Economic Council (NEC) ta ce akalla zunzurutun makudan kudaden da suka kai Naira tiriliyan takwas ne suka zurare daga manyan ma'aikatun dake tara kudade ga gwamnatin tarayya su kusan 16 daga shekarar 2010 zuwa 2015.

Ma'aikatun dai kamar yadda muka samu sun hada da NNPC, Kwastam, hukumar tashoshin ruwa, hukumar tara haraji ta kasa, hukumar tashoshin jiragen sama da dai sauran su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel