An bankado wata badakalar Naira tiriliyan 8 a manyan ma'aikatun gwamnatin Buhari

An bankado wata badakalar Naira tiriliyan 8 a manyan ma'aikatun gwamnatin Buhari

Majalisar tattalin arziki a Najeriya watau National Economic Council (NEC) ta ce akalla zunzurutun makudan kudaden da suka kai Naira tiriliyan takwas ne suka zurare daga manyan ma'aikatun dake tara kudade ga gwamnatin tarayya su kusan 16 daga shekarar 2010 zuwa 2015.

Ma'aikatun dai kamar yadda muka samu sun hada da NNPC, Kwastam, hukumar tashoshin ruwa, hukumar tara haraji ta kasa, hukumar tashoshin jiragen sama da dai sauran su.

An bankado wata badakalar Naira tiriliyan 8 a manyan ma'aikatun gwamnatin Buhari
An bankado wata badakalar Naira tiriliyan 8 a manyan ma'aikatun gwamnatin Buhari

KU KARANTA: Siyasa na neman lalata maka imani - PDP zuwa ga Osinbajo

Legit.ng ta samu cewa gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Dankwambo ne dai ya sanarwa da manema labarai hakan jim kadan bayan sun kammala taron su wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya shugabanta.

A wani labarin kuma, Babban Sakataren kasar tarayyar Amurka Mista Mike Pompeo ya kira shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a waya inda kuma ya kara jaddada cikakken goyon bayan sa da na kasar su ga shugaban da kuma Najeriya.

Mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar a Najeriya Heather Nauert ita ce ta bayyana hakan ga manema labarai inda kuma tace kasar ta Amurka ta yi jinjina ga shugaban kasar musamman ma game da irin salon mulkin sa da kuma kyakkyawan jagorancin da yake yi a nahiyar Afrika baki daya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel