Raba kayan yin shushana: Gwamnan jihar Borno ya aikawa kwamishinan sa takardar sammaci
Gwamnan jihar Borno dake a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya Alhaji Kashim Shettima a ranar Alhamis mun samu cewa ya aike da takardar sammaci tare da karin bayani zuwa ga kwamishin harkokin ilimi mai zurfi a jihar.
Gwamnan ya dai aike ta takardar ne zuwa ga kwamishinan kuma dan takarar zama dan majalisar tarayya a jihar Usman Jaha (Babawo) bisa wani abun kunya da ya ja wa jihar na rabawa al'ummar mazabar sa kayan wankin takalma.
KU KARANTA: Matsayar Buhari game da kasar Falasdinawa
Legit.ng ta samu cewa raba kayan wankin takalman dai da kwamishinnan yayi ya jawo cece-kuce tare da mabanbantan ra'ayoyi daga 'yan Najeriya da suka kalli abun a matsayin wani kaskanci.
A wani labarin kuma, Farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya yanzu haka ta kai kusa dalar Amurka 80 a karon farko tun a shekarar 2014, kusan shekaru 4 kenan biyo bayan takaddamar da ke cigaba da wanzuwa tsakanin kasar Amurka da Iran.
Mun samu daga majiyar mu ta Brent crude dai ta bayyana cewa farashin kuma zai iya ya cigaba da hawa idan dai har rashin jituwa a tsakanin kasashen biyu masu arzikin man ta cigaba da wanzuwa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng