Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya halarci Tafsiri a yau, 1 ga watan Ramadana
A yanzu haka shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yana halartan Tafsirin Al-Kur'ani mai girma a yau 1 ga watan Ramadana, 1439 AH wanda yayi daidai ga 17 ga watan Mayu, 2018.
Shugaban kasan ya halarci karatun ne a masallacin fadar shugaban kasa da ke Aso Rock, babban birnin tarayya, Abuja.
Daukacin Musulmai a fadin Najeriya da duniya ga baki daya sun waye gari ya da azumin watan Ramadan mai falala.
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Sarkin musulmi ya tabbatar da ganin watan a jihohi da dama kuma hakan a bisa al'ada na nufin watan na Ramadana ya tsaya kenan.
Legit.ng dai ta samu cewa kasar Saudiyya ma ta bayar da sanarwar ganin jinjirin watan na Ramadana a kasar ta biyo bayan fakuwar da yayi ba'a gan sa ba a jiya.
Shi dai watan Ramadana yana da matukar falala a rayuwar musulmi inda suka yadda cewa Ubangiji Allah yana bude kofofin aljanna tare da rufe na wuta a lokacin.
Haka ma dai a watan Ramadana, musulmai kan kame bakin su daga cin abinci ko shan abin sha tare da kusantar iyali daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng