Allah wadarar: Sun kashe makwabcinsu domin sace masa babur
Jami’an ya sandan jihar Ogun sun cika hannu da wanu matasa biyu wadanda suka hallaka makwabcinsu suka sanya gawarsa cikin buhu.
Makasan masu suna Patrick Udom,dan shekara 35, daga jihar Akwa Ibom da kuma James Roland, 25, dan jihar Delta sun hada baki wajen kashe makwabcinsu, Happy Patrick, ne a Imodi-Imosan.
Rahotannin sun bayyana cewa bayan kashe shi, sai suka sace babur dinshi kirar Baja kuma suka boye gawarsa cikin buhu; suka jefa cikin daji.
Kakakin hukumar yan sandan, Abimbola Oyeyemi, wanda ya bayyanawa manema labarai wannan labara yace daya daga cikin makasan, Udom, ne ya bayyanawa hukuma abinda ya faru.
Kakakin yan sandan yace sun kashe makwabcin na su ne domin samun saukin dauke babur dinsa. Ya ce jami’an yan sanda sun nemo gawan inda suka jefa shi cikin buhu a cikin daji.
Kakakin ya kara da cewa an samu makamai irinsu addauna 2, guduma, da kuma gatari da sukayi amfani da shi wajen kashe mutumin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng