Yanzu Yanzu: Sojoji sun kai hari ofishin yan sanda sun kama, DPO
- An samu rikici a kan hanyar Ada George dake garin Port Harcourt a ranar Alhamis da safe sakamakon sojoji da suka kori ofishin ‘Yan Sanda na Rumukpakani, saboda wani dan Sanda da ya kashe wani soja
- Sojan da aka kashe wanda yake cikin farin kaya an kashe shi ne a kusa da ofishin ‘Yan Sandan, inda daya daga cikin ‘yan sandan masu aiki a lokacin ya halbeshi da bindiga
- Hakan yayi sanadin da wasu daga cikin sojojin dake garin suka harzuka suka inda darkaki ofishin ‘yan sandan suka kama shugaban ofishin da kuma wanda yayi kisan
An samu rikici a kan hanyar Ada George dake garin Port Harcourt a ranar Alhamis da safe sakamakon sojoji da suka kori ofishin ‘Yan Sanda na Rumukpakani, saboda wani dan Sanda da ya kashe wani soja.
Sojan da aka kashe wanda yake cikin farin kaya an kashe shi ne a kusa da ofishin ‘Yan Sandan, inda daya daga cikin ‘yan sandan masu aiki a lokacin ya halbeshi da bindiga.
Hakan yayi sanadin da wasu daga cikin sojojin dake garin suka harzuka inda suka darkaki ofishin ‘yan sandan suka kama shugaban ofishin da kuma wanda yayi kisan.
KU KARANTA KUMA: Ana nan dai jiya Iyau: Gungun yan bindiga sun far ma kauyukan Birgin Gwari guda 4
A baya Legit.ng ta ruwaito cewa hukumar Sojojin Najeriya tace Sojoji a shirye suke a birnin tarayya da fuskantar kungiyar ‘yan Shi’a masu cigaba da gudanar da zanga-zangar tayar da hankali a birnin tarayya akan tsare shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
Kwamandan guards Brigade, Brigadier-Janar Umar Tama Musa, ya bayyana haka a wurin bude gasar motsa jini ta sojojin a birnin tarayya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng