Kwankwaso ba zai iya hana shugaba Buhari cin kano ba – Inji El-Rufa'i
Gwamna Nasir El-Rufai ya yi ba'a ga wasu kusoshin jam'iyyar APC ke barazanar barin jam'iyyar inda yace barin jam'iyyar tasu ba zai hana Shugaban kasa Muhammadu Buhari lashe zabe ba a 2019.
A kwanan nan ne wasu manyan 'yan siyasa da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC a 2014 suka yi zargin cewa an mayar da su saniyar ware tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya musu bukatunsu ba.
Sai dai Gwamna eE-Rufa'i ya yi masu hannunka mai sanda inda yace barinsu jam’iyyar ba zai hana shugaban kasar kawo jihohinsu a 2019 ba.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata, El-Rufai, ya ce "tun shekarar 2003 shugaban ke lashe zabe a Kano."
Ya cigaba da cewa idan aka yi duba ga yawan mutanen da suka fito saboda tarban Buhari, za a ga cewa Kano wuri ne da shugaban ya ke da magoya baya sosai.
Ya kuma ce, hakan ya faru ne ba tare da jama'ar Kwankwaso ba.
KU KARANTA KUMA: EFCC ta damke wani Sanata da ya karbi motocin naira miliyan 303 daga hannun barayin gwamnati
Daga karshe gwanan ya ce akwai bukatar duba korafe-korafen da manyan jam'iyyar ta APC suka gabatarwa uwar jam'iyyar da idon basira saboda siyasa, "harka ce da ke bukatar karuwar jama'a ba raguwa ba."
Ahalin da ake ciki, Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaba Buhari wanda ya yi gaisuwa ga Musulman Najeriya dama na duniya baki daya yayinda suka fara azumin Ramadana wanda ke shafe tsawon kwanaki 30 ya bayyana cewa watan Ramadan ya kasance lokaci da maida hankali ga ibadah da kuma nutsuwa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng