Yan bindiga dadi sun bude wuta akan wani na hannun daman Aliko Dangote

Yan bindiga dadi sun bude wuta akan wani na hannun daman Aliko Dangote

Gungun wasu yan bindiga sun hallaka wani babban jami’i a kamfanin simintin Dangote dake kasar Habasha, a ranar Laraba 16 ga wata Mayu, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban jami’in da ba a bayyana sunansa bay a gamu da ajalinsa ne a yankin nan da yayi kaurin suna wajen tashe tashen hankula, yankin Oromiya, yayin da yake kan hanyar dawowa daga kamfanin.

KU KARANTA: Idan da arziki da kwanciyar hankali: Karanta rahar da Dangote ya yi ma abokinsa attajiri

Wannan yanki na Oromiya ya shiga halin tashin tashina ne sama da shekaru biyu da suka gabata, sakamakon ganin da matasan yankin suke yi na cewa gwamnatin habasha ta mayar dasu saniyar ware.

Yan bindiga dadi sun bude wuta akan wani na hannun daman Aliko Dangote
Kamfanin

Gwamnatin kasar ta bayyana cewa: “An kashe daraktan kamfanin ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga kamfaninsu, tare da wasu ma’aikatan kamfanin guda biyu, a yanzu haka jami’an tsaro na bin sawun maharani.”

A yayin hare haren, yan bindigar sun kona wasu daga cikin motocin kamfanin. A shekarar 2015 ne Aliko Dangote ya kaddamar da fara aikin kamfanin simintin, wanda a duk kasar babu kamfani kamarsa.

Rikicin kasar Habasha ya kara ruruwa ne tun bayan da tsohon shugaban kasa Hailermarian Desalegn ya yi murabus, inda tuni tsohon shugaban dakarun hafsan kasa Abiy Ahmed ya dare madafan iko, amma kata kata bata rabu da kasar ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng