Abubuwa 5 da yawancin Jama’a ke tunanin suna karya azumi alhalin kuma basa yi

Abubuwa 5 da yawancin Jama’a ke tunanin suna karya azumi alhalin kuma basa yi

Akwai wasu abubuwa da Musulmai da dama masu azumi ke zaton suna karya azumi alhalin kuma a shari’ance ba haka suke ba.

Don haka muka yi amfani da wannan dama wajen jero maku wasu abubuwa da ko da anyi su basa karya azumi.

Abubuwa 5 da yawancin Jama’a ke tunanin suna karya azumi alhalin kuma basa yi
Abubuwa 5 da yawancin Jama’a ke tunanin suna karya azumi alhalin kuma basa yi

Ga su kamar haka:

1. Turare: Komai karfin turare da kamshin sa ba ya karya azumi inji Malamai. Malaman Musulunci sun ce muddin ba a sha turaren ba babu damuwa. Kwalliya a jiki ma bai isa karya azumi ba.

2. Habo ko da kaho da rana tsaka bai halatta ba amma habo idan ya zo wa mutum bai nufin azumin sa ya karye. Sai dai Malamai sun ce a guji hadiyar jinin. Haka kuma dibar jini domin ayi gwaji bai karya azumi.

3. Runguma da sumbatar mace: Don mutum ya kai ga rungumar matar sa ko ya sumbance ta a cikin watan Ramadan bai karya azumi muddin ba a kai makura wajen tada sha’awa ba. Fitan ruwan da maniyyi ba bai nufin azumi ya karye.

4. Dandana abinci: Mai azumi zai iya dandana abincin da ake shiryawa na buda-baki. Abin da bai halatta ba dai shi ne a hadiye abinci. Haka kuma goge baki bai karya azumi sai an hadiyi man gogewar.

KU KARANTA KUMA: Shugaban hukumar ‘Yan Sanda na kasa ya zargi Saraki da son janye hankali daga lamarin ‘yan ta’addan da aka dauka haya

5. Mafarki Mafarkin mace ko makamancin sa ma bai karya azumi. Mai azumin zai yi wankan janaba ne ya cigaba da azumin sa ba tare da wani ramuwa ba inji Malamai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng