Karshen duniya: Wani dan shekara 19 ya dirkawa 'yar shekara 13 ciki a garin Legas

Karshen duniya: Wani dan shekara 19 ya dirkawa 'yar shekara 13 ciki a garin Legas

Wani yaro mai shekaru 19 a duniya mai suna Friday Oyedele an zarge shi da laifin dirkawa wata 'yar yarinya mai shekaru 13 a duniya wadda aka bukaci a sakaya sunan ta ciki.

Kamar dai yadda muka samu, an dai gurfanar da yaron ne a gaban wata kotun majistare ta garin Ikeja, jihar Legas gaban babbar alkaliyar kotun Uwar gida Sule Amzat.

Karshen duniya: Wani dan shekara 19 ya dirkawa 'yar shekara 13 ciki a garin Legas
Karshen duniya: Wani dan shekara 19 ya dirkawa 'yar shekara 13 ciki a garin Legas

KU KARANTA: An ga watan Ramadana a Najeriya - Sarkin musulmi

Legit.ng ta samu cewa ita kuma da take yanke hukunci, alkaliyar ta bayar da umurnin a cigaba da tsare wanda ake zargin har sai ta kammala tuntuba da kuma neman shawara daga na gaba da ita.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar hukumar hana fasa kwauri ta tarayyar Najeriya dake a shiyyar dake kula da yanki na A karkashin shugabancin Mohammed Uba a ranar Laraba ta sanar da samun nasarar cafke motocin alfarma akalla 30 da kudin su ya kai darajar Naira biliyan 1.

Kamar dai yadda rundunar ta bayyana, an kama motocin ne lokacin da ake kokarin shigowa da su ta kan iyakar Najeriya da kasashen jamhuriyar Kamaru da Benin a jahohin Legas da Ogun dukkan su a shiyyar kudu maso yammacin kasar nan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel