An kashe ‘Yan Sanda uku a jihar Sokoto, sannan kuma an sace wani dan kasar waje
- Hukumar ‘Yan Sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kisan wasu jami’an ‘Yan Sanda uku da kuma sace wani dan kasar Syria, Abul Nasir, mai aiki da kamfanin gine-gine na Triacta Construction Company
- ‘Yar Sanda mai kula da harkokin jama’a Cordelia Nwawe, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7.20 na safe, a wurin da kamfanin ke gudanar da wani aiki a kauyen mazaru dake karamar hukumar Bodinga
- Miss Nwawe tace an tabbatar da cewa ‘Yan Sandan dake gadin waurin aikin sun mutu bayan an kaisu asibiti domin a dubasu sannan kuma wanda ke kula da aikin dan kasar ta Syria an saceshi zuwa inda ba wanda ya sani
Hukumar ‘Yan Sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kisan wasu jami’an ‘Yan Sandan uku da kuma sace wani dan kasar Syria, Abul Nasir, mai aiki da Triacta Construction Company.
‘Yar Sanda mai kula da harkokin jama’a Cordelia Nwawe, ta bayyanawa NAN, cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7.20 na safe, a wurin da kamfanin ke gudanar da wani aiki a kauyen mazaru dake karamar hukumar Bodinga.
Miss Nwawe tace an tabbatar da cewa ‘Yan Sandan dake gadin waurin aikin sun mutu bayan an kaisu asibiti domin a dubasu sannan kuma wanda ke kula da aikin dan kasar ta Syria an saceshi zuwa inda ba wanda ya sani.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa kotu ta bayar da belin Dino Melaye
NAN ta ruwaito cewa wadansu jami’an tsaro dake kula da wurin sunce wasu ‘yan ta’adda hudu ne suka zo wurin cikin mota mai bakin gilashi suka kaiwa ‘Yan Sandan hari, suka kuma tafi da Manajan wurin dan kasar Syria.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng