Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin jefa Jonah Jang Kurkuku
Jastis Daniel Longji na babban kotun Jos ya bada umurnin garkame tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah David Jang, a kurkuku.
Gabanin gabatar da wannan shari’a, Jastis Daniel Longji ya yi watsi da bukatar lauyan Jang, Robert Clarke, na belinsa kuma ya dakatad da zaman zuwa ranan Alhamis, 24 ga watan Mayu.
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa a yau aka gurfanar da tsohon gwamnan jihar Plateau Jonah David Jang gaban babbar kotu a jihar da misalin karfe 9:28am na safe.
Gwamnan dai an kawo shi harabar kotun ne cikin Mota kirar Toyota Hiace bisa rakiyar jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da kuma jami’an ‘yan sanda.
KU KARANTA: ‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma - Inji ‘Yan Shi’a
An gurfanar da shi ne kan laifuka 12 na rashawa da almundahanan N6.3 billion.
An gurfanar da shi ne tare da wani ma’ajin ofishin sakataren gwamnatin jihar, Yusuf Pam wanda ya wawuri, N11 miliion.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng