Ramadan: Matar shekarau ta tallafawa mabukata da kuma zawarawa
- Matar tsohon gwamnan jihar Kano Hajiya Halima Ibrahim Shekarau, ta bayar da tallafin kayan abinci ga zawarawa, mabukata da kuma tsofaffin mata a jihar Kano
- Abubuwan da ta raba sune buhunan shinkafa sama da 150, buhunan sikari 50, buhunan gero 50, sai kuma katan 100 na taliya
- Kayayyakin an rabawa mutane mazauna kusa da gidan tsohon gwamnan jihar dake kan hanyar Mundubawa a yankin jihar
Matar tsohon gwamnan jihar Kano Hajiya Halima Ibrahim Shekarau, ta bayar da tallafin kayan abinci ga zawarawa, mabukata da kuma tsofaffin mata a jihar Kano.
Abubuwan da ta raba sune buhunan shinkafa sama da 150, buhunan sikari 50, buhunan gero 50, sai kuma katan 100 na taliya. Kayayyakin an rabawa mutane mazauna kusa da gidan tsohon gwamnan jihar dake kan hanyar Mundubawa a yankin jihar.
Hajiya Halima wadda akafi sani da Garkuwar Nakasassu, ta bayyanawa manema labarai cewa wannan rarraba ta sabayinta duk shekara.
Ta kuma bukaci mata masu hannu da shuni na jihar dasu taimakawa talakawa da mabukata, saboda hakan zai kawo saukin wahalhalun da mutane ke fuskanta cikin wannan watan na Ramadan.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Zanyi murabus nan da mako guda – Fayemi
A halin da ake ciki, a gobe Alhamis, 17 ga watan Mayu ake sanya ran Musulmai a fadin duniya zasu fara azumin watan Ramadana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng